@ Danjuma Katsina
A yau Lahadi 10 ga watan Yuli, Alhaji Danlami M. Kurfi, tsohon Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kurfi da Dutsinma, ya jagorance mu zuwa Daura don yi wa Shugaban Kasa barka da Sallah da kuma gaisuwa.
Muna tare da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani. A Katsina muna tare da Babangida Nasamu da Injiniya Hassan Sani Jikan Malam da sauran mutane 10, duk da ni wanda na je a matsayin dan jarida.
Mu kadai muka zauna da Shugaban Kasa a wani falonsa, bayan da mai taimaka masa na musamman, Alhaji Tunde Sabi’i ya yi mana iso. Wanda ya fito kafin mu shiga, shi ne Ministan Sadarwa, Farfesa Ali Pantami.
Ni yadda na ga Buhari garau yake, domin raha da dariya aka yi ta yi da shi, har da barkwanci.Duk maganarsa ta kishin kasa ce. Mutane biyu suka yi magana. Daga Alhaji Danlami Kurfi, sai Kakakin Majalisar Jihar Kaduna. Sai Babangida M. Nasamu, tsohon Dan Majalisar Jihar Katsina ya rufe taron da addu’a. Aka daki hotuna, muka koma gidan Alhaji Musa Haro Dan Madamin Daura, inda nan muka fara sauka muka ci abincin rana.
A gidan Buhari Na hadu da Alhaji Mansir, wanda ya ce, “Alhaji Danjuma! Yanzun nan tare da minista muka karanta rahoton musamman da kuka rubuta a kan kai wa tawagar Shugaban Kasa hari.”
“Duk abin da kuka rubuta,jami an tsaro sun tabbatar da hakan, Good with your investigative journalism”
Danjuma , shi ne mawallafin jaridun Katsina City News, Taskar Labarai da The Links News.